News
Tankar Mai Ta Kuma Faduwa A Niger Inda Mutane Sunje Ɗiban Ganima.
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Tankar mai ta kuma faduwa jihar Niger, inda mutane suka je ɗiban ganima, kwanaki biyu bayan irin wannan abu ya afku da yayi sanadiyyar mutuwar mutane 96.
Motar man fetur din ta fadi a yau litinin a birnin Bida.
Wani faifan bidiyon da yake yawo a kafafen sada zumunta ya nuna yadda matasa ke kokarin kwasar man dake kwarara daga motar dakon man.
Sai dai wasu mutanen sun gudu daga wajen da motar ta fadi don gujewa faruwar makamancin iftila’in da ya afku ranar asabar a yankin Dikko Junction.
Wani mai suna Yunusa, da jaridar Premium Times, ta zanta dashi ya bayyana mamakin sa akan yadda mutane basa jin tsoron motar ta kama da wuta.
-
News1 day ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News2 days ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
