Connect with us

News

‎Wata Tankar Gas Ta Murƙushe Adaidaita Sahu ‎ ‎

Published

on

FRSC 768x576

‎Wani mutum ya rasa ransa a wani mummunan haɗarin mota da ya faru a mahaɗar Immigration Junction da ke Agu Awka, a kan titin Awka zuwa Enugu a Jihar Anambra.

‎Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11 na safe a ranar Laraba, inda wata tankar gas ta yi karo da wata adaidaita sahu

Advertisement

Farashin Kaya Ƙaru Zuwa Kashi 15.38 A Najeriya

‎Rahotanni sun nuna cewa direban adaidaita sahun ya mutu nan take bayan da tankar, wadda ke ɗauke da gas mai yawa, ta murƙushe shi.

Advertisement

‎Shaidun gani da ido sun ce direban adaidaita sahun na ƙoƙarin wucewa ne daga wajen jami’an tsaro da ke karkatar da zirga-zirga sakamakon aikin gyaran hanya, a lokacin da tankar ta samu matsalar birki.

‎Jami’ar hulɗa da jama’a ta Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC) a Jihar Anambra, Margaret Onabe, ta tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa.

Advertisement

‎Ta ce mutane biyu lamarin ya rutsa da su inda direban adaidaita sahun ya rasu, yayin da direban tankar ya tsira ba tare da rauni ba.

‎A cewarta, matsalar birki ce ta haddasa haɗarin bayan direban tankar ya kasa sarrafa motar.

Advertisement

 

 

Advertisement

PUNCH

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending