News
JIGAWA:Makiyaya A Gwaram Sun Zargi Hakimin Fagam Da Tauye Haƙƙoƙinsu Tsawon Shekaru 20
Wasu makiyaya Fulani mazauna Rugar Waja da ke yankin Fagam a ƙaramar hukumar Gwaram, jihar Jigawa, sun zargi Hakimin Fagam, Alhaji Auwalu, da tauye musu haƙƙoƙinsu tare da nuna musu rashin adalci na tsawon sama da shekaru ashirin.
Makiyayan sun bayyana cewa sun daɗe suna fuskantar matsin lamba a yankin, inda suka ce ana hana su ‘yancin gudanar da harkokinsu na kiwo da noma cikin kwanciyar hankali.
Kwankwaso Ya Ce Bai Yanke Shawara Kan Makomar Siyasarsa Ba Har Yanzu
Hardo na yankin, Alhaji Isma’il Usman, ya shaida cewa ana tilasta musu fitar da zakka daga dabbobinsu da kuma amfanin gonarsu ba tare da yardarsu ba, duk da yawan koke-koken da suka ce sun dade suna kaiwa hukumomi.
“Mun shafe lokaci mai tsawo muna kai koke kan wannan lamari amma babu wani sauyi. Muna ganin ana tauye mana haƙƙinmu ne kai tsaye,” in ji shi.
Shi ma wani makiyayi, Alhaji Bello Usman, ya bayyana cewa matsalar ta shafi batun gadon iyaye, inda ya ce matasa a yankin ba sa samun damar mallakar gadonsu yadda ya kamata bisa tanadin addini.
“Yaranmu ba sa samun haƙƙin gadon iyayensu kamar yadda addini ya tanada, wannan babbar damuwa ce a gare mu,” in ji Bello.
Sai dai da aka tuntubi Hakimin Fagam kan zarge-zargen, ya ce ba shi da hurumin yin magana a kai, tare da ba da shawarar a tuntubi hukumomin da abin ya shafa domin karin bayani.
Makiyayan sun yi kira ga gwamnatin jihar Jigawa da sauran hukumomin da abin ya shafa da su shiga lamarin cikin gaggawa, domin tabbatar da adalci da kare haƙƙoƙin al’ummar yankin.
