News
KOGI: Ana Zargin Dangin Ɗalibi Sun Kashe Malamar Makaranta Saboda Ta Ladabtar da Shi

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kogi ta kaddamar da bincike kan mutuwar wata malamar makaranta, Maryam Usman, wadda ake zargin ta rasa ranta bayan an kai mata hari saboda ladabtar da wani ɗalibi a makaranta.
Rahotanni sun ce marigayiyar, wadda ke koyarwa a wata makarantar firamare da ke yankin Olamaboro na jihar, ta hukunta wani ɗalibi ne bisa laifin rashin ɗa’a. Sai dai daga baya mahaifin ɗalibin tare da wasu mutane ake zargin sun kai mata hari, inda suka yi mata mummunan duka har ta samu munanan raunuka.
An garzaya da ita asibiti domin ceto rayuwarta, amma daga bisani ta rasu sakamakon raunukan da ta samu, lamarin da ya jawo alhini da fushin al’umma da kuma ƙungiyoyin malamai.
Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kogi ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda ta ce jami’an tsaro sun fara bincike tare da farautar waɗanda ake zargi, bayan sun tsere kafin isowar jami’an ‘yan sanda. Ta kuma bayyana cewa za a mika lamarin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka (CID) da zarar an kama waɗanda ake nema.
Lamarin ya tayar da hankulan al’umma, inda ake kira ga hukumomin tsaro da su tabbatar an yi cikakken bincike tare da hukunta duk wanda aka samu da hannu a wannan al’amari domin tabbatar da adalci ga marigayiyar.
