News
Gobara Ta Kone Dakin Kwanan Dalibai Mata A Kano
Wata gobara ta kone dakin kwanan ɗalibai mata a makarantar Dano Memorial da ke ƙaramar hukumar Sumaila a jihar Kano, inda ta yi sanadin lalacewar kayan ɗalibai da dama.
Lamarin ya faru ne da daren Litinin, a lokacin da ɗaliban suka tafi hutu, kamar yadda jami’in hulɗa da jama’a na ƙaramar hukumar Sumaila, Malam Gunduwawa, ya tabbatar a cikin wata sanarwa da ya fitar.
Yadda ‘Yan Bindiga Sun Mayar Da Sama Da Mutane 6,000 ‘Yan Gudun Hijira A Katsina
Gobarar ta kone dakin kwanan gaba ɗaya, inda ta lalata kayan ɗalibai da suka haɗa da tufafi, littattafai da sauran muhimman abubuwa. Sai dai, rahotanni sun tabbatar da cewa ba a samu asarar rai ba.
Shugaban ƙaramar hukumar Sumaila, Farouk Abdu, ya kai ziyarar gani da ido zuwa makarantar, inda ya jajanta wa shugabannin makarantar da kuma ɗaliban da abin ya shafa.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
