Connect with us

News

Yadda ‘Yan Bindiga Sun Mayar Da Sama Da Mutane 6,000 ‘Yan Gudun Hijira A Katsina

Published

on

IMG 20250730 WA0002

Fiye da mutane 6,000 ne suka tsere daga muhallansu tare da neman mafaka a sassa daban-daban na ƙaramar hukumar Bakori da kewaye, sakamakon hare-haren da ‘yan bindiga ke ci gaba da kai wa a wasu kauyuka na jihar Katsina.

Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun addabi kauyuka sama da goma da ke zagaye da Bakori, inda suka kashe mazauna yankunan, suka sace wasu, sannan suka tursasa wa dubban jama’a yin hijira domin tsira da rayukansu.

Ma’aikatan Jinya Da Ungozoma Sun Fara Yajin Aiki A Najeriya

Kauyukan da suka fi fuskantar wannan annoba sun hada da Guga, Kandarawa, Kakumi, Monono, Unguwar ‘Yar Dabaru, Unguwar Ɗan Marka, Sabon Gida da kauyen Doma, tsakanin sauran su.

Jaridar AMINIYA ta ziyarci wasu daga cikin wuraren da ‘yan gudun hijirar suka fake a garin Bakori, ciki har da makarantar firamaren Nadabo da unguwannin Kafaɗi da Ma’aru da ke Sabuwar Abuja. A can ya iske daruruwan mata da ƙananan yara na tsugunne a gidajen ‘yan uwa da abokai, wasu kuma a makarantu.

Wani daga cikin waɗanda suka tsira daga harin, Imrana Shafi’u daga kauyen Ɗan Marka, ya shaida wa wakilinmu cewa ‘yan bindigar sun harbe shi a ƙafafu har sau biyu. “Da suka zo kanmu harbi kawai suka fara yi. Ni ma sai da suka harbe ni sau biyu a ƙafa. Na zaci mutuwa ta yi gaba da ni, sai Allah ya kare ni,” in ji shi.

Ita kuwa Malama Marawiya, wacce ta tsere daga kauyen ‘Yar Dabaru, ta bayyana cewa ‘yan bindigar sun yi awon gaba da mata fiye da goma, yawancinsu suna dauke da jarirai a bayansu. “Yanzu kwana goma kenan suna da su a daji, kuma suna neman a biya Naira miliyan daya da rabi akan kowanne mutum kafin su sako su,” ta bayyana cikin damuwa.

Advertisement

Yusuf Usman daga kauyen Doma, wanda ke zaune a sansanin makarantar Nadabo, ya ce kimanin mutane dari uku suka tsere tare, ciki har da tsofaffi. “Muna tafiya a ƙafa har zuwa Bakori tare da yara da mata, saboda babu abin hawa,” in ji shi.

A cewarsa, “Tun sama da shekaru biyar muke cikin wannan hali na rashin tsaro. Ko da dare ko da rana, a kowane lokaci ana shigowa garuruwanmu ana kashe mutane ko kuma a sace su a kai da su daji domin neman kudin fansa.”

Shugaban Kwamitin kula da ‘yan gudun hijirar a ƙaramar hukumar Bakori, Malam Mamman Yaro Bakori, ya tabbatar da cewa mutane fiye da 3,500 ne ke neman mafaka a Bakori, yayin da sama da 2,500 ke zaune a garin Guga.

Ya ce, “Yawan ‘yan gudun hijirar kullum ƙaruwa yake yi, domin ana cigaba da kai hare-hare a kauyukan da ke kewaye. Wasu na zaune a gidajen ‘yan uwansu, wasu kuma a makarantar Nadabo.”

Shugaban karamar hukumar Bakori, Abubakar Barde, ya ce sun fara raba kayan abinci sau uku a rana ga ‘yan gudun hijirar, tare da basu tallafin kudin cefane domin rage radadin da suke ciki.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending