News
Gwamnan Kano Ya Ba Da Umarnin Gyaran Makarantar Koyon Faransanci Da Chinese
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayar da umarnin a gaggauta gyara Makarantar Koyon Harsunan Faransanci da Sinanci da ke Kwankwaso, a karamar hukumar Madobi, domin inganta ilimi da bunkasa koyon harsuna a jihar.
Wannan umarni na Gwamna Abba na zuwa ne bayan wata ziyarar bazata da ya kai makarantar a farkon makon nan, inda ya duba yadda ake gudanar da karatu da koyarwa a cikin makarantar.
NAFDAC Ta Rufe Wasu Shaguna A Kano, Ta Cafke Mutum 6 Kan Sayar Da Man ‘Bleaching’
A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida na jihar, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya fitar, Gwamna Abba ya bayyana gamsuwarsa da kwazon malamai da daliban makarantar, musamman yadda daliban ke iya amfani da harshen Faransanci da na Sinanci cikin kwarewa.
“Na je na gani da idanuna yadda ake gudanar da harkokin makarantar. Na ji daɗin irin jajircewar da malamai da dalibai ke nunawa, musamman yadda suke iya mu’amala da harsunan Faransanci da Sinanci,” in ji Gwamnan.
Gwamnan ya ce ganin halin da ginin makarantar ke ciki, ya umarci Kwamishinan Ayyuka na jihar da ya gaggauta fara aikin gyaran sassan da suka lalace domin bai wa dalibai da malamai ingantaccen yanayi na karatu.
Sanarwar ta bayyana cewa wannan mataki na daga cikin shirin gwamnatin Kano na inganta bangaren ilimi, musamman wajen samar da ingantattun makarantu da kayan koyarwa domin bunkasa kwarewar dalibai a fannin harsuna.
Gwamnatin Kano ta ce tana da kudurin ci gaba da daukar matakan da suka dace domin ciyar da harkar ilimi gaba a jihar.
