Connect with us

News

Maulidi Ba Wurin Miyagun Ɗabi’u Ba Ne – Zawuyiyar Sheikh Tijjani Usman

Published

on

IMG 20260810 WA0020

Zawuyiyar Sheikh Tijjani Usman Zangon Barebare ta yi kira ga matasa da su kiyaye mutuncin zaman Maulidin Annabi Muhammad (S.A.W.), tare da nisantar duk wani abu da zai iya lalata tarbiyya da martabar taron.

Zawuyiyar ta jaddada muhimmancin guje wa shaye-shaye, miyagun ɗabi’u da sauran abubuwan da ba su dace da zaman Maulidi ba, tana mai cewa wajibi ne mahalarta su gudanar da tarukan cikin ladabi da kamun kai.

“Na Shirya Juyin Mulki Ne Saboda Kishin Ƙasa, Ba Don Neman Mulki Ba” — Kanal Ma’aji

Ta ce Maulidin Annabi (S.A.W.) lokaci ne na tunawa da rayuwar Manzon Allah da koyarwarsa, don haka bai kamata a mayar da shi wajen aikata abubuwan da suka saba wa tarbiyyar Musulunci ba.

A cewar Zawuyiyar, ya kamata matasa su kasance abin koyi wajen kiyaye tarbiyya, ladabi da mutunta juna, musamman yayin gudanar da tarukan Maulidi.

Ta kuma yi kira ga iyaye, malamai da shugabannin al’umma da su ƙara ƙoƙarin wayar da kan matasa kan muhimmancin kiyaye tarbiyya da ɗabi’un Musulunci yayin irin waɗannan taruka.

Advertisement

Zawuyiyar ta ce kiyaye mutuncin Maulidi nauyi ne da ya rataya a wuyan kowane mahalarta, domin tabbatar da cewa tarukan sun kasance wajen ƙara soyayya ga Annabi Muhammad (S.A.W.) da koyon kyawawan ɗabi’unsa.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending