News
“Na Shirya Juyin Mulki Ne Saboda Kishin Ƙasa, Ba Don Neman Mulki Ba” — Kanal Ma’aji
Kanal Mohammed Ma’aji, jami’in Sojin Najeriya da ake zargi da jagorantar wani shirin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya ce kishin ƙasa da damuwa kan halin da Najeriya ke ciki ne suka sa ya shiga cikin shirin, ba neman mulki ko wata fa’ida ta kashin kai ba.
Ya ce matsin tattalin arziki, rashin ingantaccen shugabanci da kuma tabarbarewar jin daɗin ’yan Najeriya da jami’an tsaro sun ƙara masa damuwa kan makomar ƙasar.
Jihar Kano Ta Shiga Cikin Jerin Manyan Biranen Duniya 10 Masu Yawan Jama’a
Ma’aji ya ce matsalolin ƙasar sun shafe shi kai tsaye, musamman yadda yake fama da wahalar kula da ’ya’yansa biyar da ƙaramin albashinsa.
Ya kuma bayyana damuwarsa kan jin daɗin sojoji, musamman waɗanda suka samu raunuka yayin ayyukan tsaro, yana mai zargin cewa wasu daga cikinsu ba sa samun isasshen kulawa a Asibitin Sojoji na 44 da ke Kaduna.
A cewarsa, manufar shirin ita ce ganin an samu Najeriya mai wadata da za ta zama abin alfahari ga ’yan ƙasa. Sai dai ya ce shirin bai kai matakin aiwatar da shi ba kafin kama shi, domin suna kan matakin tattara jami’an soji masu irin wannan tunani ne, kuma ba a sanya wata rana ta musamman domin aiwatar da abin da ake zargin an shirya ba.
Kanal Ma’aji ya musanta hannun ƙasashen waje a lamarin, yana mai cewa shi ne ya ɗauki nauyin wasu daga cikin kuɗaɗen shirin, yayin da Timipre Silva ya bayar da gudunmawar kusan Naira miliyan 400.
Ya kuma yi kira da a inganta albashi, walwala, fansho da ilimin jami’an tsaro, tare da samar da hanyar da za su rika gabatar da korafe-korafinsu ba tare da fargabar tsangwama ba.
