News
Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Wani Matashi Kan Zargin Hallaka Mahaifinsa Mai Shekaru 80 A Katsina
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina ta kama wani matashi mai shekaru 27, Sada Tambai, bisa zargin kashe mahaifinsa mai shekaru 80, Adamu Tambai.
Lamarin ya faru ne a ranar 21 ga Satumba, 2026, a ƙauyen Mundadu da ke Ƙaramar Hukumar Bindawa ta jihar Katsina.
An Tsinci Wata jinjira A Masallacin Jumma’a A Argungu
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DSP Abubakar Sadiq-Aliyu, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Katsina.
A cewar sanarwar, rundunar ta samu kiran gaggawa daga Hakimin Bindawa, Dan Yusufan Katsina, cewa an samu tsohon shugaban unguwar Mundadu, Adamu Tambai, kwance ba ya motsi a wajen gidansa.
Bayan samun rahoton, jami’an ’yan sanda sun garzaya wurin da lamarin ya faru tare da kai mutumin zuwa asibiti mafi kusa. Sai dai likitan da ya duba shi ya tabbatar da cewa ya rasu kafin a fara ba shi magani.
Rundunar ta ce binciken farko ya kai ga cafke ɗan marigayin, Sada Tambai, wanda ake zargi da aikata laifin. An ce wanda ake zargin ya amsa cewa ya bugi mahaifinsa a kai da sanda.
Kakakin rundunar ya ce Kwamishinan ’Yan Sandan Katsina, Ali Umar-Fage, ya bayar da umarnin tura lamarin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jiha (SCID) domin gudanar da cikakken bincike.
Ya ce za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike, yayin da rundunar ta jajanta wa iyalan marigayin tare da tabbatar da cewa za ta tabbatar da an bi doka wajen gudanar da binciken.
