Connect with us

News

Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Gonakin Shinkafa Sama Da 200 A Kano

Published

on

2

Ambaliyar ruwa ta lalata gonakin shinkafa sama da 200 a yankin Shuwaki, da ke Ƙaramar Hukumar Tudun Wada ta Jihar Kano.

Ambaliyar ta biyo bayan ruwan sama mai ƙarfi da aka samu a yankin, wanda ya mamaye gonakin tare da lalata amfanin gona, lamarin da ya jefa manoma cikin babbar asara.

Jirgin Sama Ya Yi Saukar Gaggawa A Saudiyya Bayan Da Matuƙan Suka Kaure Da Faɗa

Baya ga gonakin, ambaliyar ta kuma lalata wata tsohuwar gada da ke kan hanyar Tudun Wada zuwa Shuwaki, lamarin da ya kawo cikas ga zirga-zirgar jama’a da kayayyaki.

Halin da ake ciki ya ƙara dagula rayuwar mazauna yankin, musamman manoman da ke dogaro da noman shinkafa wajen samun abin masarufi da kuɗin shiga.

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta gaggauta tallafa wa manoma da sauran mutanen da ambaliyar ta shafa, domin rage musu radadin asarar da suka yi.

Advertisement

Majalisar ta kuma bukaci a ɗauki matakan gaggawa wajen gyara gadar da ta lalace, domin dawo da zirga-zirga a kan hanyar Tudun Wada zuwa Shuwaki.

 

 

PUNCH

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending