Connect with us

News

Gwamnatin Tarayya Ta Fara Shirin Samar Da Wutar Lantarki Ta Sa’o’i 24 A Kano Da Wasu Birane 2

Published

on

Wutar Lantarki

Gwamnatin Tarayya ta fara tattaunawa da kamfanonin rarraba wutar lantarki kan shirin samar da wutar lantarki ta sa’o’i 24 a manyan cibiyoyin kasuwanci da masana’antu, ciki har da Lagos, Abuja da Kano.

Wutar za ta kasance ne domin amfanin gidaje, ‘yan kasuwa da masana’antu a manyan yankunan kasar da bukatar wutar lantarki ta yi yawa.

Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Gonakin Shinkafa Sama Da 200 A Kano

Jaridar PUNCH ta rawaito cewa Ministan Wutar Lantarki, Joseph Tegbe, ya gana da shugabannin wasu kamfanonin rarraba wutar lantarki domin tattauna shirin.

Shirin ya fi mayar da hankali ne kan yankunan Lagos; Abuja-Kaduna-Kano; da Enugu-Port Harcourt.

A cewar sanarwar da mai taimaka wa ministan kan harkokin yada labarai, Adeola Adelabu, ya fitar ranar Laraba, manufar shirin ita ce inganta samar da wutar lantarki da kuma tabbatar da cewa wutar da ake samarwa da kuma isar da ita zuwa layin kasa ta isa ga masu amfani cikin sauki.

Advertisement

Ministan ya bayyana cewa matsalar wutar lantarki a Najeriya ba ta tsaya ga samar da wuta da isar da ita kadai ba, domin akwai kuma matsalar yadda kamfanonin rarraba wutar ke karbar wutar da kuma isar da ita ga masu amfani.

Ya ce samar da yankunan makamashin zai taimaka wajen rage wannan matsala, tare da kara samar da damar amfani da wutar ga harkokin kasuwanci da masana’antu.

Gwamnatin Tarayya ta kuma ce za ta ci gaba da fadada ababen more rayuwa na wutar lantarki a wuraren da bukatar wutar ta yi yawa, domin samar da wuta da ta dace da bunkasar tattalin arzikin kasar.

Sai dai gwamnatin ba ta bayyana lokacin da za a fara aiwatar da shirin ba, ko adadin wutar da za a samar wa kowane yanki.

Shirin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun korafe-korafe kan rashin tabbas wajen samun wutar lantarki da kuma yadda kamfanonin rarraba wuta ke isar da wutar da ake da ita ga masu amfani.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending