Connect with us

News

Jami’an Yansanda Sun Kama Wadanda A Ke Zargi Da Garkuwa Da Mutane 24 Da Kwato Makamai A Kaduna

Published

on

Rundunar ƴan sanda a Kaduna ta ce ta kama mutane 24 da a ke zargi da garkuwa da mutane, tare da ƙwato bindigogi 24, ciki har da AK-47 guda uku da ɗaruruwan harsashi.

Kwamishinan ƴan sanda a jihar, Muhammad Rabiu, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Kaduna. Ya ce an samu nasarorin ne ta hanyar amfani da bayanan sirri, sa ido da kuma haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro da ƙungiyoyin tsaron al’umma.

Gwamnatin Tarayya Ta Fara Shirin Samar Da Wutar Lantarki Ta Sa’o’i 24 A Kano Da Wasu Birane 2

Daga cikin abubuwan da a ka kwato akwai bindigogi kirar gida, harsasan AK-47 guda 270 da na Type-06 guda 30. Haka kuma, ƴan sanda sun ce sun daƙile wani harin ƴan bindiga a Maƙarfi, inda suka kama wani da a ke zargi tare da ƙwato bindiga, harsasai.

Kwamishinan ya ce a na ci gaba da farautar wasu da ake zargi da hannu a safarar makamai da sauran laifuka, tare da kira ga jama’a da su rika kai rahoton duk wani motsi da ake zargi ga jami’an tsaro.

 

Advertisement

DAILY TRUST 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending