Connect with us

News

’Yan Bindiga Sun Hallaka Hakimin Da Suka Sace A Kano

Published

on

Hukumomi a Najeriya sun tsaurara matakan tsaro da kuma sa ido sosai a birnin Kano,

Ƴan bindiga sun kashe basaraken da ke jagorantar ƙauyen Aujarawar Alkali da ke ƙaramar gukumar Gezawa a Kano, Alhaji Ahmad Yakubu Ahmad.

A na zargin masu garkuwa da mutane ne su ka kasheshi bayan sun sace shi.

Jami’an Yansanda Sun Kama Wadanda A Ke Zargi Da Garkuwa Da Mutane 24 Da Kwato Makamai A Kaduna

Rahotanni sun ce Ahmad ya shiga hannun masu garkuwa ne a ranar Talata, 17 ga Satumba 2026, bayan wasu ƴan bindiga sun mamaye al’ummar ƙauyen da daddare.

Daga bisani, an gano gawarsa bayan masu garkuwar sun kashe shi. An gudanar da sallar jana’izarsa da misalin ƙarfe 3 na yammacin Laraba, sannan aka binne shi.

Wani mazaunin Gezawa, Musa Garba, ya tabbatar da faruwar lamarin ga wakilin jaridar ta wayar tarho.

Advertisement

Garba ya ce maharan sun azabtar da dagacin har lahira, inda suka yanke masa ƙafa ɗaya sannan suka ɗaure masa hannayensa a bayansa.

Ya ce daga bisani masu garkuwar sun binne gawar dagacin a wani kabari mara zurfi a wani ƙauye mai suna Danladin Gezawa.

Garba ya ce ya halarci sallar jana’izar dagacin da misalin ƙarfe 3 na yammacin Laraba. Ya bayyana cewa maharan sun azabtar da dagacin sosai har ya mutu.

A cewarsa, bayan mutuwar dagacin, masu garkuwar sun binne gawarsa a kabari mara zurfi a Danladin Gezawa. Bayan kwanaki huɗu, wasu mazauna ƙauyen su ka gano kabarin tare da sanar da lamarin.

Ya ce matar marigayin ce ta tabbatar da cewa gawar da aka gano ta mijinta ce. Daga nan aka kai gawar asibiti, inda jami’an asibitin su ka tabbatar da mutuwarsa, kafin daga bisani a binne shi saboda gawar ta fara rubewa.

Har yanzu rundunar yan sanda a Kano ba su ce komai a kan labarin ba.

Advertisement

 

AMINIYA

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending