Uncategorized
NAPTIP Ta Bankaɗo Yunƙurin Safarar Mutane 1,508

Hukumar Yaƙi da Safarar Mutane ta Ƙasa (NAPTIP) ta bayyana cewa ta gano yunƙurin safarar mutane 1,508 tare da kama mutum 1,434 da ake zargi da hannu a wannan aika-aika tsakanin watan Agustan 2025 zuwa yanzu.
Darakta-Janar ta hukumar, Binta Bello, ce ta bayyana hakan yayin taron tuntubar masu ruwa da tsaki kan yaƙi da safarar mutane karo na 29, da kuma taron tsara manufofi karo na uku, wanda aka gudanar a Abuja.
ADC Ta Kafa Kwamitin Yakin Neman Zaben Gwamna A Kano
A cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na Facebook ranar Talata, Bello ta ce NAPTIP ta kuma karɓi tare da ba da kulawa ga mutum 2,700 da suka faɗa tarkon safarar mutane a cikin wannan lokaci.
Ta ƙara da cewa hukumar ta gurfanar da mutum 85 a gaban kotu, bisa tuhume-tuhume 65 da suka shafi safarar mutane.
A cewarta, wasu shari’o’i 74 sun ƙare da samun nasarar yanke wa mutum 97 hukunci kan laifukan safarar mutane.
Darakta-Janar ɗin ta bayyana cewa tun bayan kafa hukumar, ta samu nasarar ceto mutum 28,762 daga hannun masu safarar mutane, tare da tabbatar da hukunta mutum 857 da aka samu da aikata laifukan.
Bello ta ce hukumar na ƙara ƙaimi wajen amfani da fasahar zamani wajen yaƙi da safarar mutane, musamman ta intanet, da sauran hanyoyin yaudarar mutane da cin zarafinsu.
Ta kuma jaddada muhimmancin inganta tattara bayanan sirri, kare waɗanda suka faɗa tarkon masu safarar mutane da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashe domin kawo ƙarshen matsalar.
Haka kuma, ta yi kira da a gaggauta kafa rundunar NAPTIP a Jihar Delta, wadda ta ce ita ce jiha ɗaya tilo a ƙasar da har yanzu ba ta da rundunar hukumar.
A cewarta, kafa rundunar a jihar zai taimaka wajen ƙarfafa yaƙi da safarar mutane da kuma inganta hanyoyin kare waɗanda wannan mummunar sana’a ta shafa.
-
Labarai7 days ago
Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Yi Wa Masu Digirin Ƙasashen Waje Jarrabawa
-
Labarai3 days ago
Jami’an Tsaro A Pakistan Sun Kama ’Yan Najeriya 20 Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi
-
Labarai2 days ago
Hare-haren Ta’addanci Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 835 A Najeriya Cikin Wata Guda – Rahoto
