Sports
Najeriya ta sha kashi hannun Portugal 4 – 0
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Ƙungiyar kwallon ƙafa ta Najeriya, Super Eagles ta sha kashi a hannun Portugal da ci huɗu da nema.
Super Eagles ta sha kashi ne a wani wasan sada zumunta da ya gudana ranar Alhamis da daddare.
An fara zura wa Najeriya ƙwallo ne a minti tara da fara wasa ta hannun Bruno Fernandes.
Sannan aka ƙara wa Najeriyar a minti na 35 ta hanyar fanareti, wadda Fernandes ɗin ya buga.
Sauran ƙwallaye biyu da aka jefa a ragar Najeriya sun zo ne bayan dawowa hutun rabin lokaci.
Gonçalo Ramos ne ya zura ƙwallo ta uku a minti na 82, sannan bayan minti 2, João Mário ya cike ƙwallo ta huɗu a minti na 84.
-
News4 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News7 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News6 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
