Connect with us

Sports

Fitaccen dan kwallon duniya, Pele ya rasu

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

Fitaccen ɗan ƙwallon nan na duniya ɗan ƙsar Brazil, Pele ya rasu yana da shekara 82.

Advertisement

Pele ya rasu ne a ranar Alhamis 29 ga watan Disamban 2022 bayan ya sha fama da rashin lafiya.

A kwanakin baya an yi ta yaɗa labarin ƙarya na rasuwarsa.

Advertisement

Ya rasu ne sakamakon cutar kansar ƙaba da kuma cutar ƙoda

Gwamnan Legas ya gana da sifeton ‘yan sanda kan kisan lauya

Advertisement

Ana ganin Pele shi ne ɗan ƙwallon da ba a taɓa samun irin sa ba a duniya, kuma sau uku yana cin gasar kofin duniya wa ƙasarsa Brazil.

Ya ci kofin duniya a shekarun 1958 da 1962 da kuma 1970.

Advertisement

A shekarar 2000 ne kuma hukumar ƙwallon ƙafar duniya FIFA, ta ayyana shi a matsayin ɗan ƙwallon ƙarni.

Shi ne ɗan ƙwallon da ya kafa tarihin zura ƙwallaye 1,281 a raga a cikin wasanni 1,363 cikin shekara 21 da ya yi yana buga tamaula.

Advertisement

Cikin waɗannan har da ƙwallo 77 da ya ci wa ƙasarsa cikin wasanni 92 da ya buga wa Brazil ɗin.

An yi wa Pele tiyata a kan yanke masa kansa a hanjinsa a watan Satumban 2021 a Asibitin Albert Einstein da ke Sao Paulo.

Advertisement

An sake kwantar da shi a asibiti a watan Nuwamban 2022.

Ƴarsa Kely Nascimento ta yi ta sanar da masoya halin da mahaifinta ke ciki a shafukan sada zumunta daga asibitin da yake jinya.

Advertisement

A ranar Alhamis ɗin ta wallafa wani hoto da ke nuna hannayen iyalan Pelen a kan jikinsa a asibiti inda ta rubuta: “Muna maka godiya kan duk abin da ka yi mana. Muna matuƙar ƙaunarka. Allah Ya ji ƙanka.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending