News
Sojojin Amurka da Koriya ta Kudu da Japan na atisayen kwana biyu
Sojin ruwan ƙasashen Koriya ta Kudu da Amurka da Japan na gudanar da atisayen kwanaki biyu, domin inganta aikinsu.
A wani mataki na tauna tsakuwa kan barazanar hare-haren makamai masu linzami na Koriya ta Arewa.
Bayan shekaru 9 da Aure ba haihuwa: Matar Aure ta haifi ‘ya’ya 5 rigis
Manufar Tisayen shi ne faɗaɗa ikonsu da horon da zai ba su damar kare teku kan hare-haren makaman nukiliya na ƙarƙashin teku da Arewar ta fara yi a baya-bayan nan.
Za su samu horo kan yadda za su iya gano makamin nukiliya da zarar an sanya shi cikin teku.
Inda za a sanya wasu motocin teku na musamman a matsayin kan-da-garki.
Advertisements
