News
Manoman tumatur a jahar Kano sun yi asarar kusan biliyan 2 saboda wata tsutsa
DAGA JAMILA MUHAMMAD IBRAHIM
Kimanin manoman tumatur dubu biyar a Kano sun rasa inda za su sa kansu saboda wannan ibtila’in na tsutsar da ta cinye musu gona.
Manoman tumatir a jihar Kano sun tafka asarar sama da Naira biliyan 1 da biliyan 500 kuma har yanzu suna ci gaba da kidayar asarar wadda wata shu’umar tsutsa ta haddasa musu.
Tsutsar da ake kira ‘Tuta Absaluta’ ta lalata gonakan tumatiri da dama, lamarin da ya durkusar da manoman sama da dubu biyar a jihar.
Wannan ibtila’in ya haifar da karancin tumatur a sassan jihar Kano da kewaye.
Ko a shekarar da ta gabata jaridar indaranka ta ruwaito cewa a karamar hukumar Rogo an samu wannan ibtila’in na tsutsa inda mazauna yanke suka sama ta suna ‘sharunan’
Advertisements
