Politics
Duk Kadarorin Gwamnati da aka siyarwa da gidan Ganduje sai mun karbo su – Baffa Bichi
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Shugaban kwamitin karbar mulki na jam’iyyar NNPP, Dakta Baffa Bichi ya jagoranci kwamitin kwato kadarorin Gwamnati da ake zargin an siyar zuwa ofishin hukumar Public Procurement Agency bayan zargin cewa an cefanar da hukumar dan gidan Gwamna mai barin Gado, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.
Baffa Bichi yayi gargadin cewa za su baiwa Gwamnati mai shigowa shawarar hukunta duk wanda ya siyar da wurin da ma wanda ya rusa ofishin.
Advertisements
