Connect with us

Politics

yaki da talauci  na  daya daga cikin manyan abubuwan da ya sa a gaba—-Umar Namadi

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

Gwamnan jihar Jigawa, mai jiran Gado Mallam Umar Namadi, ya ayyana yaki da talauci  na  daya daga cikin manyan abubuwan da ya sa a gaba idan ya karbi ragamar mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023.

Ya bayyana hakan ne ga manema labarai jim kadan bayan samun rahoton kwamitin mika mulki na gwamnatin jihar.

Advertisement

Wakilin Nasara Radio a jahar jigawa Muhammad Sa’idu Limawa ya rawaito cewar zababben gwamnan, ya bayyana cewar gwamnati mai ci ta kashe biliyoyin Naira wajen karfafawa da samar da ayyukan yi da sauran kayan aikin kawar da fatara da rage radadin talauci a fadin jihar.

Hukumar EFCC sun kama tsohon ministan lantarki Saleh Mamman

Mallam Umar Namadi ya ci gaba da bayyana cewa, a sakamakon dauki-ba-dadin da gwamnatin tarayya da ta jiha da sauran masu ruwa da tsaki suka yi, ya sa an samu raguwar talauci a jihar.

Advertisement

Zababben Gwamnan ya kuma bayyana rashin amincewar sa kan rahotannin da aka samu daga Cibiyar Kiwon Lafiyar Jama’a ta kasa da ta bayyana jihar Jigawa a cikin jerin jahohin da ke fama da talauci a Najeriya, inda ya ce hakan ba gaskiya ba ce.

 

Advertisement

Ya yi nuni da cewa, yawancin kananan kwamitoci sun riga sun mika rahotonsu ga babban kwamitin mika mulki na jihar ta jigawa kuma dukkan tsare tsare suna tafiya yadda ya kamata.

 

Advertisement

Zababben gwamnan wanda kuma shi ne mataimakin gwamnan jihar mai ci, ya nanata kudurinsa na ci gaba da aiwatar da dukkan kyawawan manufofi da tsare-tsare da gwamnatin Gwamna Badaru ta fara domin ci gaban jihar, da zamantakewa da tattalin arziki.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending