Politics
In Tinubu Ya Bani Minista Bazan Karba Ba Saboda Na Tsufa Da Yin Rushe-Rushe – El Rufa’i
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufai ya ce idan zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Tinubu ya masa tayin zama minista a gwamnatin sa, bazai karba ba.
El-Rufai ya bayyana hakan ne a birnin tarayya Abuja, yayi da yake jawabi lokacin kaddamar da wani littafi.
Ana ganin kalaman na gwamna El-Rufai a matsayin martani ga jita-jitan da ake yi na cewa, Bola Tinubu zai nada shi a matsayin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, ko kuma Ministan Birnin Tarayya Abuja.
El-Rufai wanda ya yi ministan birnin tarayya Abuja tun a tsohuwar gwamnatin tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo, ya sha bayyana cewa a yanzu bashi da bukatar muƙamin minista.
Da yake jawabi a wurin taron kaddamar da wani littafi El-Rufai ya ce “na yi aikina na gama. Ni in na gama da abu na gama da shi kenan. Ba na waiwaye.”
“Ko lokacin da na bar ma’aikatar birnin tarayya, ban sake komawa ba sai sau daya a 2016. Shi ma lokacin da aka naɗa abokina da muka yi karatu da shi a matsayin minista, kuma yace yana so ya ganni a wurin”
“Da zaran na gama da aiki, bana waiwaye. Idan na bar gidan gwamnatin Kaduna nan da kwana 19 masu zuwa, ba abinda zai sa na koma sai in wani dalili da ya zama wajibi.”
“Saboda haka ni bana tunanin kujerar ministan Abuja, ba ma na maganar akan wadanda suka zo a bayana ma. Kamar yadda na fada in ma an bani, bazan karba ba.”
“Ni fa bana maimaita aji. Akwai matasa masu jini a jika da zasu iya wannan aikin. Za ma su iya wanda ya fi nawa”
“Ni na tsufa yanzu. Na tsufa da rushe rushe. Ku je ku nemo matashi ko matashiya mai jini a jika. Amma ni bana so” a cewar El-Rufai.
