Connect with us

News

Kungiyar Oldboys ta Yabawa Gwamnan Kano Bisa Matakin Rusa Shaguna da Gine-ginen da akayi a Harabar Makarantu a Jahar

Published

on

Daga Faruk Muhammad, Kano

 

Advertisement

Kungiyar Daliban Sakandaren Gwamnati ta kasa Goron Dutse Oldboys ta yabawa Gwamnan Jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf bisa matakin da ya dauka na rusa shaguna da gine-ginen da aka gina a harabar makarantar da kewaye da gwamnatin da ta gabata ta Dr. Abdullahi Umar Ganduje ta gudanar.

Kafin wannan lokaci dai a baya kungiyar ta yi Allah wadai da yadda gwamnatin da ta gabata ta Dr. Ganduje ta sayar da harabar makarantun gwamnati ga wasu ‘yan kasuwa marasa kishin kasa wadanda ba su da sha’awar ci gaban ilimi a jihar kano ba.

Advertisement

Yanzu Kanawa za su tabbatar suna da Gwamna==Tijjani Makwarari

Kungiyar Oldboys ta kasa ta bayyana goyon bayanta ga rusa haramtattun gine-ginen da ke kewayen makarantun gwamnati ta hannun jami’in hulda da jama’a Comrade Salisu Ismail Kabuga.

Yakara da cewa muna fatan Allah ya kawo gwamnatin da za ta ceto makarantun ‘ya’yan talakawa, wanda gwamnatin da ta shude ta hada baki da ‘yan kasuwa da ba su da sha’awar ilimi domin a lalata su.

Advertisement

Da yake zantawa da manema labarai a inda GSS Goron Dutse dake kan titin FCE Kano, a ranar Lahadi, Kakakin kungiyar na kasa, Kwamared Salisu Kabuga ya ce, “Lokacin da gwamnatin Mai Girma Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje ta fara siyar da makarantar .yan kasuwa, kungiyar ta tashi tsaye wajen jawo gwamnati kan illolin da ke tattare da sayar da harabar makarantun amma ta toshe kunnuwanta”.

Kakakin GSS Goron Dutse na kasa ya kara da cewa, “Gwamnatin da ta shude ta yaudari kungiyoyin tsofaffin dalibai wajen siyar da kewayen makarantun da abin ya shafa domin inganta yanayin makarantun, kuma babu wani abu da ya canza ko inganta harkar ilimi a makarantunmu. amma sai ya kara tabarbarewa, da fatan za a kyautata yanayin makarantun a karkashin jagorancin gwamnan jihar na yanzu Engr. Kabir Yusuf.

Advertisement

Sai dai Kwamared Salisu Kabuga ya bukaci gwamnatin jihar da ta kara himma wajen inganta harkar ilimi ta hanyar kawo makarantun Kano da suka lalace a baya tare da samar da dukkanin abubuwan da ake bukata domin ci gaba da gudanar da ingantaccen koyo da koyarwa. .

Ya kuma ba da tabbacin gwamnati na bayar da hadin kai da goyon bayan dukkanin kungiyoyin da ke Kano domin cimma manufofin da gwamnati mai ci ta gindaya na inganta harkokin ilimi a jihar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending