Labarai
Za’a Yiwa ‘Yansanda Masu Bada Hannu Akan Titi Karin Girma

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Sufeton rundunar ‘yansanda ta kasa Usman Alkali Baba, Ya bada umarnin tantance kwazon jami’an rundunar dake aikin bada hannu akan titina da kula da zirga-zirgar ababen hawa, domin yi masu karin girma zuwa matsayi na gaba.
Wata sanarwa da kakakin rundunar, CSP Olumiyiwa Adejobi ya fitar a jiya, Ta ce aikin tantacewar wani bangare ne na yiwa jami’an karin girma.
Kungiyoyin ASUU Da ASUP Sunce Babu Tabbas Wajen Aiwatar Da Dokar Bada Lamunin Karatu
Ya ce sufeton yansandan na kasa ya bada umarnin daga likafar jami’an yansandan masu aikin bada hannu da suka dace bisa la’akari da kwazonsu wajen aiki, da kuma shaidar karatu da suke da shi, zuwa matsayi na gaba.
Kakakin ‘yansandan na kasa, Ya ce wannan wani bangare ne na kokarin da rundunar ta take na samarwa da jami’an ta cigaban da ake bukata.
-
Labarai6 days ago
Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Yi Wa Masu Digirin Ƙasashen Waje Jarrabawa
-
Labarai2 days ago
Jami’an Tsaro A Pakistan Sun Kama ’Yan Najeriya 20 Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi
-
Labarai2 days ago
Hare-haren Ta’addanci Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 835 A Najeriya Cikin Wata Guda – Rahoto
