Connect with us

News

Rusau: Mun Kwato Filayen Tiriliyan din Nairori – Dakta Baffa Bichi

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

 

Advertisement

Sakataran Gwamnatin jihar Kano, Dakta Baffa Bichi, ya ce gwamnatin jihar ta kwato filaye da darajarsu ta kai tiriliyan nairori tun bayan da ta fara aikin rusau a wasu wurare a jihar kano.
Gwamnatin jihar karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta rusa wasu gine-gine a otal din Daula, filin Idi na Kano, kasuwannin Kwari da Wambai da dai sauransu.

An ƙaddamar da dokar ta-ɓaci kan satar waya a Kano

Ta zargi gwamnatin da ta shude da yin sama da fadi da dukiyar kasa, amma tsohon gwamnan, Abdullahi Umar Gnaduje, ya bayyana zargin a matsayin maras tushe.

Advertisement

Dokta Bichi, a wata hira da gidan talabijin na Channels TV’s  a shirin Politics Today, ya ce, “Wani yana ikirarin an ruguza gine-gine na Naira biliyan 129.
“Mun kwato kadarori (filaye) na jihar Kano na tiriliyan naira da gwamnatin da ta gabata ta karkatar da kansu da iyalansu. Filin Idi kadai ya kai tiriliyan nairori. Ba shi da kima.”

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending