News
Rusau: Mun Kwato Filayen Tiriliyan din Nairori – Dakta Baffa Bichi
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Sakataran Gwamnatin jihar Kano, Dakta Baffa Bichi, ya ce gwamnatin jihar ta kwato filaye da darajarsu ta kai tiriliyan nairori tun bayan da ta fara aikin rusau a wasu wurare a jihar kano.
Gwamnatin jihar karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta rusa wasu gine-gine a otal din Daula, filin Idi na Kano, kasuwannin Kwari da Wambai da dai sauransu.
Ta zargi gwamnatin da ta shude da yin sama da fadi da dukiyar kasa, amma tsohon gwamnan, Abdullahi Umar Gnaduje, ya bayyana zargin a matsayin maras tushe.
Dokta Bichi, a wata hira da gidan talabijin na Channels TV’s a shirin Politics Today, ya ce, “Wani yana ikirarin an ruguza gine-gine na Naira biliyan 129.
“Mun kwato kadarori (filaye) na jihar Kano na tiriliyan naira da gwamnatin da ta gabata ta karkatar da kansu da iyalansu. Filin Idi kadai ya kai tiriliyan nairori. Ba shi da kima.”
-
Opinion7 days ago
Tiriliyan ₦210 na Karya: Yadda Bala Wunti Ya Warware Dukkan Rudanin da Ya Mamaye Zaman Majalisar Dattawa Kan Asusun NNPC
-
News5 days ago
Likitan El-Rufai Ya Shiga Matsala Kan Zargin Bayar Da Rahoton Jinya Na Bogi
-
News3 days ago
Uba Ya Nemi Kotu Ta Tilasta Wa ’Yarsa Ta Fitar Da Mijin Aure A Kaduna
