News
Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta rufe gidajen mai guda biyar
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.
Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa mai kula da harkokin man fetur ta rufe gidajen Mai guda biyar bisa laifin damfarar kwastomomi.
Shugaban Taskforce, Kanar Muhammad Alhassan (Rtd) ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan ya duba wasu gidajen mai a kananan hukumomin Kiyawa, Gumel, da Jahun.
Yarima Munir Ja’afaru, Ya Miƙa Takardar Murabus ɗinsa na Hakimin Basawa.
Ya ce an duba ayyukan gidajen man ne domin tabbatar da sun bi ka’idojin da aka gindaya.
Alhassan ya bayyana cewa, Taskforce ta yi gargadin sama da gidajen mai talatin (30) tare da rufe biyar (5) saboda yin wasu ayyukan da ba su dace ba.
Ya ce kwamitin zai ci gaba da duba sauran gidajen mai tare da fallasa duk wani gidan mai da aka samu yana damfarar mitoci don rage masu mu’amala da su.
-
News4 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News6 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News6 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
