News
Yan Nijeriya miliyan 62 ne za su amfana da shirin ‘cash transfer’ – Betta Edu
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa, ‘yan Nijeriya miliyan 62 ne za su amfana daga shirin ba da tallafi na “Conditional Cash Transfer” inda kowanne zai riƙa samun tallafin kuɗi na N25,000 duk wata har na tsawon wata uku.
Kazalika, gwamnatin ta yi alkawarin tallafa wa mata ‘yan kasuwa su miliyan ɗaya da rabi ta shirin “Iyaloja Fund”.
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya sake sabbin nade-naden mukamai
Ministar Jinƙai da Yaƙi da Talauci, Dr Betta Edu ce ta bayyana haka sa’ilin da ta kai wa Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris Malagi, ziyara ranar Talata a ofishinsa da ke Abuja.
A cewarta, “Za mu aiwatar da shirye-shirye mabanbanta don kyautata rayuwar ‘yan ƙasa.
“Ta yaya za mu samar da muhalli, kula da lafiya, samar da abinci mai gina jiki ga mutane miliyan 16 da rikici ya shafa? Akwai buƙatar mu tallafa wa waɗan nan mutane, wasunsu ‘yan gudun hijira ne wanda matsalar tsaro ta ɗaiɗaita, wasunsu kuma iftila’i ne, kamar ambaliya, ya raba su da matsuguninsu
“Akwai shirye-shirye da dama da muka samar da nufin cire ‘yan Nijeriya daga ƙangin talauci, akwai shirin yaƙi da yunwa wanda ya ƙunshi ciyar da ɗaliban makaranta da raba tallafin kuɗi.
“Shugaba Tinubu zai tallafa wa magidanta miliyan 15 wanda ya yi daidai da mutum miliyan 62 da kuɗi N75,000, wato Naira dubu 25 duk wata har na wata uku,” in ji ta.
A nasa ɓangaren, Alhaji Malagi ya bai wa Ministar tabbacin samun goyon bayan ma’aikatarsa, yana mai cewa yaƙi da talauci shi ne mabuɗin bunƙasar tattalin arziki.
Bayan tarin jawabai masu kama hankali da ya yi, Malagi ya bai wa takwararsa tabbacin za su yi aiki tare don cimma kyawawan manufofin gwamnatin Shugaba Tinubu.
Wani labarin kuma Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya sake sabbin nade-naden mukamai
Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya ayyana yau Laraba 4 ga watan Oktoba 2023 a matsayin ranar hutu domin zagayowar ranar takutaha da ake murnar tunawa da ranar sunan haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W.
Sanarwar hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida Alhaji Baba Halilu Dantiye ya fitar a safiyar yau Laraba.
Gwamnan ya bukaci al’ummar jihar da su yi amfani da lokacin domin yin tunani a kan koyarwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da sanya su cikin harkokinsu na yau da kullum.
Ya kuma bukaci jama’a da su rika yin addu’o’in samun zaman lafiya da ci gaba a Kano da Najeriya baki daya.
Ya yi addu’ar Allah ya shiga al’amuranmu a wannan lokaci mawuyaci, ya kuma bamu albarkacin wannan damuna da kuma lokacin mai zuwa.
