Connect with us

News

An Gurfanar Da Mutane 14 Kan Karyar Bacewar Mazakuta A Birnin Tarayya Abuja 

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, Abuja ta ce ta gano ba gaskiya ba ne rahoton da wasu mazauna yankin 14 suka yi cewa an sace musu mazakuta ba.

Advertisement

Kwamishinan ‘yansandan babban birnin tarayya, Haruna Garba, ya ce an gano rahoton ba gaskiya ba ne, bayan da aka duba lafiyar wadanda abun ya shafa.

Yan Nijeriya miliyan 62 ne za su amfana da shirin ‘cash transfer’ – Betta Edu

Garba ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja kan nasarorin da rundunar ta samu a yaki da miyagun laifuka.

Advertisement

Ya kara da cewa mutane 14 da ke da hannu a lamarin a halin yanzu ana ci gaba da bincike a kansu bayan an tabbatar da karyar da suka yi.

“Ana tuhumar su da bayar da bayanan karya da kuma tayar da hankalin jama’a.

Advertisement

“Sun yaudari ‘yansanda wajen tunkarar wani harin da aka kai kan sama da mutane 10 da ake zargi a birnin tarayya a cikin ‘yan makonnin da suka gabata.”

 

Advertisement

Garba ya ce an sanar da ‘yansandan rahotanni sama da 10, galibinsu a kewayen Garshi, Gwagwalada da Kwali da ke cikin babban birnin tarayya Abuja, inda ya ce wasu daga cikin wadannan rahotanni ba su da tushe.

 

Advertisement

Sai dai shugaban ‘yansandan ya ce ba a samu asarar rai ba a lamarin ba.

 

Advertisement

“Rundunar ‘yansandan babban birnin tarayya Abuja ta tattara rahotanni sama da 10 da ake zargi da bacewar mazakutar maza a fadin yankin da kuma kara ta’azzara rikicin da matasa masu fusata ke yi.

 

Advertisement

“Rundunar ‘yansanda ta dauki matakin hana asarar rayuka da dukiyoyi da kuma dawo da doka da oda.

 

Advertisement

“Mutane 14 da ake zargi da cewa bacewar mazakutar tasu, an kai su asibiti inda likitan ya tabbatar da cewa sassan jikin nasu yana kuma suna aiki.

“Saboda haka, an gurfanar da su gaban kotu da laifin bayar da bayanan karya da kuma tayar da hankalin jama’a,” in ji shi.

Advertisement

Garba ya yi kira ga mazauna yankin da su gargadi ‘ya’yansu da su daina tayar da hankulan jama’a.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending