News
Shari’ar Gwamnan Kano: Ma’aikatar Shari’armu Tana Bukatar Gyara, -PICaN
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Wata kungiya mai rajin tabbatar da dimokaradiyya mai suna Partnership for Issues-Based Campaign in Nigeria (PICaN) ta yi kira da a yi wa tsarin shari’ar Najeriya garambawul, biyo bayan abin da ta kira da rashin adalci da kotun sauraron kararrakin zabe ta jihar Kano ta yi a kwanan baya.
Damuwa da hukuncin da kotun sauraren kararrakin zabe ta yanke kan al’amuran da suka zaben Kano da kuma wasu bayanai da ke ci gaba da bayyana gazawar INEC a cikin ayyukanta da kundin tsarin mulkin kasar nan.
Haka kuma kungiyar tace tsarin zaben, muna kira da a amince da cikakken rahoton kwamitin zabe na mai shari’a Muhammad Uwais, wanda ya ba da shawarar hanyoyin da idan aka aiwatar da su za su inganta tsarin zabe baki daya tare da karfafa tsarin shari’a da kuma inganta ‘yancin gudanar da zabe.
Buguda kari Wani shine buƙatar rufe ɓangarorin ta hanyar gyara sashe na 64 (4), (5) na Dokar Zaɓe ta 2022 (kamar yadda aka gyara) game da watsa bayanan amincewa da aka rubuta, kuri’u da sakamakon zaben da aka rubuta”.
“Saboda haka, akwai bukatar a yi gyara cikin gaggawa domin tilasta wa INEC mika sakamakon zabe ta hanyar lantarki daga rumfunan zabe a kan lokaci wanda zai inganta sahihancin zabe da tattara sakamako”.
Shugaban kungiyar PICaN na kasa, Kwamared Bako Abdul Usman ya bayyana hakan a ranar Laraba a Kaduna, ya ce doka ya kamata ta zama fata ta karshe ga kowani talaka, don haka ne ake sa ido a kan bangaren shari’a don taka muhimmiyar rawa wajen dorewar wannan dimokuradiyya.
kuma bai kamata a yi la’akari da ita a matsayin cibiyar da ke yin zagon kasa ba.
Ya kamata hukumomin tsaro su fahimci cewa zanga-zangar wata hanya ce da ‘yan kasa ke bayyana ra’ayinsu da burinsu, don haka ya kamata hukumomin su ba da fifiko wajen gudanar da bincike kan wadanda aka kama domin a sako su.
Ya kara da cewa ya zama wajibi, fiye da kowane lokaci, a tantance koke-koke da kararrakin zabe kafin a rantsar da dan takara.
yayin da ya yi kira ga dukkan bangarorin da ke korafi da su daina barin magoya bayansu su dauki doka a hannunsu.
