News
An Hana Sayar Da Littafin Queen Primer A Fadin Jihar Kano
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Shugaban hukumar tace fina-finai da dab’i ta jihar Kano, Abba El-mustapha, ya bayyana cewa, hukumar ta hana Sayarda Littafin Queen Primer kuma hanin ya fara nan take.
El-Mustapha ya bayyana cewa, hukumar a karkashin jagorancinsa ta kama kwafi fiye da 1,200.
Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun kakaba dokar hana fitar da Makamashin iskar Gas zuwa kasashen waje
ya kara da cewa, Babban dalilin dakatar da Sayarda Littafin shi ne, korafe-korafen da aka gabatar wa hukumar cewa, littafin yana bata tarbiyyar yara.
Don haka, daga yanzun, an hana sayarda wannan littafi a duk fadin jihar Kano.
Wani labarin kuma Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun kakaba dokar hana fitar da Makamashin iskar Gas zuwa kasashen waje
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
