News
Babban Jojin Najeriya Ya Ce Babu Barazanar Da Zata Hana Alkalai Yin Aiki Da Doka
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Babban jojin Najeriya mai shari;a Olukayode Ariwoola ya ce babu wata suka duk zafinta ko wani ra’ayin jama’a da zai sa bangaren shari’a ya yi wasu abubuwa da suka ci karo da kundin tsarin mulkin kasa, a shari’oin dake gaban kotunan kasar nan.
Alkalin Alkalan na kasa ya ce wajibi ne Alkalai su yi aiki da doka a lokacin da suke yanke hukunci akan kowacce irin shari’a a kasar nan.
Gwamnatin Tarayya Zata Maida Motoci Milyan 10 Masu Amfani Da Man Fetur Zuwa Gas
Mai shari’a Ariwoola ya baiyana haka ne a ranar Laraba lokacin da yake rantsar da sabbin alkalan babbar kotun tarayya guda 23, wanda daga cikinsu hadda dansa mai suna Olukayode Ariwoola.
Ya kuma yi gargadin cewar ba za’a saurarawa duk wani alkali da aka samu da yin ba daidai ba a lokacin zaman shari’a.
Y ace hukumar shari’a ta kasa zata dauki mataki mai tsauri akan Alkalan da aka samu da sakaci wajen gabatar da aikinsu.
Wani labarin kuma Gwamnatin Tarayya Zata Maida Motoci Milyan 10 Masu Amfani Da Man Fetur Zuwa Gas
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
