Connect with us

News

An Yi Wa Malamar Jami’ar FUT Yankar Rago A Gidanta Da Ke Minna

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

 

An yi ma wata malamar jami’ar fasaha ta gwamnatin tarayya (FUT), da ke Minna a jihar Neja, Dakta Sherifat Funmilola Adefolalu, yankan rago a gidanta da ke Minna ranar Lahadi.

Advertisement

An gano ta kwance a mace a cikin gidanta da ke unguwar Bbaiko a Minna.

An kona zauren majalisar dokokin jihar Ribas Bayan Barazanar Tsige Gwamna

An fahimci cewa ‘yan uwa da abokan arzikinta sun yi ta ƙoƙarin nemanta ta wayar tarho amma ba su sameta tun da safiyar ranar Lahadi.

Advertisement

A lokacin da wasu da suka damu da cewa ba su ji ɗuriyarta, sun je gidanta domin neman ta kwatsam sai suka tarar da malamar a tsangayar koyar da ilimin Biochemistry kwance cikin jini.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Wasiu Abiodun, ya tabbatar wa LEADERSHIP cewa wasu abokanta sun je gidanta nemanta sakamakon cewa sun kasa samunta a waya.

Advertisement

“Abun takaici, a lokacin da masu ziyarartar nata suka shiga cikin gidanta, sun risketa kwance cikin jini ga kuma raunuka a sassan jikinta.”

Ya ce, wasu wuƙaƙe guda biyu ɗauke da jini a jikinsu da ake zargin da su ne makasan suka yi amfani wajen daddaɓa mata an samesu a inda lamarin ya faru.

Advertisement

PPRO ya ce an ɗauki gawar mamaciyar zuwa asibitin IBB inda a nan ma likita ya tabbatar da cewa ta mutu, ya ƙara da cewa tunin aka ƙaddamar da bincike domin gano makasan, ya ba da tabbacin cewa za su yi duk mai yiyu domin kamo makasan.

Shi ma shugaban ƙungiyar ASUU reshen jami’ar FUT Minna, Dakta Bolarin Gbolahan, ya tabbatar da kisan da aka yi wa mambarsu.

Advertisement

Dr Gbolahan ya koka kan cewa kusan kowa mako yanzu sai an yi garkuwa da mambobinsu a Keffi, “Rayuwar mu cikin hatsari ba mu iya barci da ido biyu. Dole a dauki mataki kafin dukkanin mu ya mu ƙare.”

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending