Connect with us

News

Shugaban mulkin sojin Nijar ya kai ziyararsa ta farko ƙasar waje

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Shugaban gwamnatin mulkin soji a Jumhuriyar Nijar Janar Abdourahamane Tchiani ya kai ziyararsa ta farko zuwa Mali.

Tchiani dai ya kai ziyarar ce domin ganawa da takwaransa na ƙasar Kanal Assimi Goita.

Advertisement

Jami’an Tsaro Sun Hana ’Yan NNPP Yin Sallar Neman Nasara A Jihar  Kano

Zai shafe sa’o’i kaɗan a Bamako a ziyarar aiki da kuma kulla abota da ya kai ƙasar.

Makwabtan Nijar ɗin da suka haɗa Mali da Burkina Faso – wadda sojoji ke jagoranta bayan kwace mulki a 2020 da kuma 2022, sun yi alkawarin goyon bayan sojojin na Nijar.

Advertisement

A watan Satumba ƙasashen uku na yankin Sahel su saka sanya hannu kan wata yarjejeniya kare iyakokin juna idan aka yi yunkurin far musu.

Sun kuma yi alkwarin karfafa dangantaka a ɓangaren tattalin arziki.

Advertisement

Sun kuma haɗa kai don yaƙi da masu iƙirarin jihadi a ƙasashensu.

A wani labarin kuma Jami’an Tsaro Sun Hana ’Yan NNPP Yin Sallar Neman Nasara A Jihar  Kano

Advertisement

Aƙalla mutum 50 ne suka mutu a yankin Tigray da kuma Amhara da ke arewacin Habasha saboda fari da ya jawo yunwa, kamar yadda jami’ai a yankin suka shaida wa BBC.

A cewar ofishin kare afkuwar bala’o’i na yankin Tigray, ya ce mutane 46 suka mutu bayan barin gidajensu da suka yi sakamakon fari.

Advertisement

Shugaban ofishin Gebrehiwot Gebregziabher, ya ce an samu mace-macen ne a garin Yechilla.

A garin Wag Hemra na yankin Amhara, akalla mutum shida ne da dabbobi 4,000 suka mutu saboda ƙarancin abinci, a cewar wani jami’i.

Advertisement

Amurka da MDD sun dakatar da kai kayan agaji zuwa Habasha tsawon watanni biyar, bayan zarge-zargen satar abinci da ake yi.

Matsalar jin kai, da yaƙi, da kuma sauyin yanayi ya jefa miliyoyin mutane dogara da agajin da ake kai wa.

Advertisement

Yayin da arewacin Habasha ke fuskantar tsananin fari, ana sa ran kudanci da kuma gabashin ƙasar za su fuskanci mamakon ruwan sama da ba a taɓa gani ba.

A cewar MDD, sama da mutane 40 ne suka mutu a baya-bayan nan, sakamakon ambaliya da kuma zaftarewar laƙa, inda da yawa daga cikinsu suka fito daga yanin gabashin Somali.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending