Connect with us

News

Rundunar ’yan sandan Jihar Jigawa ta kama mutum 26 da ake zargi da aikata kwacen Waya

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Rundunar ’yan sandan Jihar Jigawa ta kama mutum 26 da ake zargi da aikata kwacen wayoyi da kuma shan muggan kwayoyi.

Kakakin rundunar, DSP Lawan Shiisu, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Dutse.

Ina sane da sadaukarwar da kuke yi saboda sauye-sauyen gwamnati -Tinubu

Ya ce kamen ya biyo bayan wasu jerin samame da suka kai a tsakanin ranar 18 zuwa 19 ga watan Disamba, a kananan hukumomi hudu na jihar.

Kakakin ya ce jami’an rundunar sun kama wani matashi kan zargin satar waya da kuma sata kudi Naira 10,000 a garin Babura da ke Karamar Hukumar Babura.

Advertisement

Aminiya ta ruwaito cewa sun kama wasu mutum biyu kan zargin laifin satar kwamfutoci shida da babur a Hadejia.

A wani labarin kuma Ina sane da sadaukarwar da kuke yi saboda sauye-sauyen gwamnati -Tinubu

Babban Bankin Najeriya CBN ya sauya matsayarsa kan hada-hada da kuɗin intanet ko kuma cryptocurrency a ƙasar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma’a da ke umartar bankunan kasuwanci na Najeriya cewa su yi watsi da haramcin da ya saka kan amfani da kuɗin na crypto tu a 2021.

CBN ya ce yadda ake yayin kuɗin na crypto yanzu a faɗin duniya ya nuna irin buƙatar da ake da ita ta saka dokoki a kan sa.

“A watan Fabarairun 2021 CBN ya haramta wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi amfani da cryptocurrency saboda almundahanar kuɗi da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci,” in ji sanarwar.

Advertisement

“Sai dai kuma, abin da ke faruwa a duniya ya nuna cewa akwai buƙatar a kula da dukiyoyin hada-hada ta intanet wato Virtual Assets Service Providers (V/ASPs).”

Ya ƙara da cewa hukumar kula da hada-hada da hannayen jari za ta fitar dokoki da sharuɗɗan amfani da dukiyoyoin intanet ɗin.

Amma babban bankin ya jaddada haramcin yin kasuwanci, ko kuma mallakar asusun crypto ga bankunan kasuwancin su da kansu

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending