News
Sama da sojojin 50,000 ne ba za su yi kirsimeti da Iyalan su ba saboda aikin samar da tsaro a Kasa – Lagbaja
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Babban hafsan hafsan soji (COAS), Taoreed Lagbaja, ya bayyana a ranar Talata cewa sama da sojoji 50,000 ne ke gudanar da ayyukan wanzar da zaman lafiya a fadin kasar nan.
Janar Lagbaja ya bayyana hakan ne a wajen wani liyafar cin abinci na musamman da aka shirya wa sojojin runduna ta 6 ta sojojin Najeriya da ke Fatakwal.
Gobara Ta Kone Shaguna 22 Tare Kadarori Na Miliyoyin Kudi A Kasuwar Gwarzo Dake Jihar Kano
Akalla sojoji sama da 50,000 ne za su yi Kirsimeti ba tare da iyalan su ba. Suna can wuraren ain samar da tsaro a fadin kasar nan.
Premium Times ta ruwaito cewa Lagbaja ya ce 2024 zai fi shekarun baya a wajen harkar tsaron Najeriya, domin akwai shirye-shirye da tsare-tsare da ke tafe domin tsaron kasar nan.
“A cikin shekara mai zuwa, rundunar sojojin Najeriya na sa ran samun sabbin jiragen sama masu saukar ungulu da sauran makaman yaki da za a yi aiki da su wajen samar da ingantaccen yanayin tsaro a fadin kasar nan.
“Har ila yau, hedkwatar sojojin ta kaddamar da ayyukan jin dadin jama’a da dama wadanda za su shafi sojoji da iyalansu kai tsaye.
Ya kara da cewa, “Karfafa jin dadin sojoji ke kan gaba a cikin abubuwan da muka saka a gaba, kuma za mu ci gaba da yin aiki tukuru don samar wa sojoji kayan aiki da tallafi don gudanar da ayyukansu cikin sauki kuma yadda ya kamata.”
-
News3 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion6 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
