News
Yan Majalissar Dokokin Najeriya Na Shirin Katse Hutu Domin Amincewa Da Kasafin 2024
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Majalisar dattawa za ta zartas da kudurin kasafin kudin shekarar 2024 a ranar asabar 30 ga watan Disamba don dorewar tsarin kasafin kudin kasa dake farawa daga watan Janairu zuwa Disamba na kowacce shekara.
Jagoran Majalisar Dattawa, Opeyemi Bamidele ya bayyana haka a wata zantawa da ‘yan jarida a garin Iyin-Ekiti na jihar Ekiti a lokacin hutun Kirsimeti, inda ya ce duk ‘yan majalisar tarayya zasu rage hutun su domin ganin an gaggauta amincewa da kudirin kasafin kudin.
A karshe ya bayyana cewa dukkan ma’aikatu da hukumomi za su bayyana a gaban zaman hadin gwiwa na dukkanin kwamitocin da abin ya shafa na majalisar dattawa da wakilai.
A wani labarin kuma Innalillahi wa inna ilaihirraji un :Allah ya yiwa tsohon kakakin majalisar wakilai Ghali Umar Na’abba rasuwa
Babban Bankin Najeriya CBN ya sauya matsayarsa kan hada-hada da kuɗin intanet ko kuma cryptocurrency a ƙasar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma’a da ke umartar bankunan kasuwanci na Najeriya cewa su yi watsi da haramcin da ya saka kan amfani da kuɗin na crypto tu a 2021.
CBN ya ce yadda ake yayin kuɗin na crypto yanzu a faɗin duniya ya nuna irin buƙatar da ake da ita ta saka dokoki a kan sa.
“A watan Fabarairun 2021 CBN ya haramta wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi amfani da cryptocurrency saboda almundahanar kuɗi da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci,” in ji sanarwar.
“Sai dai kuma, abin da ke faruwa a duniya ya nuna cewa akwai buƙatar a kula da dukiyoyin hada-hada ta intanet wato Virtual Assets Service Providers (V/ASPs).”
Ya ƙara da cewa hukumar kula da hada-hada da hannayen jari za ta fitar dokoki da sharuɗɗan amfani da dukiyoyoin intanet ɗin.
Amma babban bankin ya jaddada haramcin yin kasuwanci, ko kuma mallakar asusun crypto ga bankunan kasuwancin su da kansu
-
News3 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion6 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
