Connect with us

News

Amarya Ta Tura A Kashe Wadda Mijinta Zai Aura Ta 3

Published

on

DAGA  MARYAM BASHIR MUSA

 

Advertisement

Ana neman wata matar aure kan zargin ta da sa kashe bazawarar da mijinta zai aura.

Wadda ake zargin ita ce matar magidancin ta biyu, kuma wadda mijinta yake son ya kara a matsayin ta uku, mijinta ne ya rasu.

Advertisement

Shugaba Tinubu ya amince a biya Super Eagles da wasu ‘yan wasan Nijeriya bashin biliyan 12

Mai sana’ar sayar da abincin a Karamar Hukumar Ilọrin ta Yamma a Jihar Kwara ta nemi a kashe bazawarar ce da nufin hana mijinta kara aure.

Matar da ake zargin ta tsere, amma an cafke dan ina-da-kisan da ta dauka haya, bayan ya je gidan bazawarar, ya nemi ta fito domin karbar kayan tallafi.

Advertisement

Bazawarar mai suna Afusat ta shaida wa wakilinmu cewa, ta sha samun kiraye-kirayen barazana daga masu neman ta fasa auren.

“Da wanda ake zargin ya zo, sai ya bukaci dole sai na bi shi, shi ne na yi masa ihun barawo, makwabta suka bi shi suka kama shi a yayin da yake kokarin tserewa, suka kwace bindiga a hannunsa,” in ji ta.

Advertisement

Afusat ta ce “Da farko na ki amincewa da bukatar ma’aurin nawa, amma daga baya na amince bayan ya dage cewa yana son in zama matarsa ta uku.

“Mijina ne ya rasu, ina da ’ya’ya, ciki har da ’yan shekaru biyar da shekaru tara, kuma ni ke daukar nauyin kula da su tun da mahaifinsu ya rasu.”

Advertisement

Aminiya ta ruwaito cewa Ta yi zargin cewa matar bazawarin nata ta sha yin barazanar tura mata ’yan daba idan ba ta rabu da mijina ba.

Daga nan sai ta roki jama‘a da gwamnatin jihar da su ba ta kariya tare da ’ya’yanta daga kisan gilla.

Advertisement

Kakakin ’yan sandan jihar, Toun Ejire-Adeyemi ta tabbatar wa wakilinmu cewa “wanda ake zargin ya amsa cewa matar mutumin ce ta biya shi N10,000 ya kashe bazwarar, kuma man kama shi da

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending