News
Tsadar Rayuwa: Jama’a Sun Daka Wa Motar Dangote Wawa A Katsina
DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO
Jama’ar gari a Jihar Katsina sun daka wa wata motar kamfanin Dangote wawa, inda suka yi awon gaba da kayan abincin da take dauke da su.
Hakan ta faru ne a yayin da matsin rayuwa da tsadar kayan masarufi a Najeriya suka kai makura, inda kudin buhun masara ya kusa ninka mafi karancin albashi.
Jami’an Rundunar Sojin Saman Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Yin Garkuwa Da Mutane A Kano
A bidiyon wasoson da ke yawo a kafofin sada zumunta, an ga maza da mata da kananan yara suna daukar buhunan kayan abinci suna awon gaba da su daga babbar motar da ke kan babbar hanya.
Wasu daga cikin mutanen kuma suna kokawar daukar buhunan abincin, da ake zargin za a kai kasar Jamhuriyar Nijar ne.
Amma a sanarwar kamfanin da ke tabbatar da aukuwar lamarin, kamfanin na Dangote ya musanta cewa Nijar zai kai kayan abincin.
Aminiya ta ruwaito cewa a shekarar da ta gabata ne Najeriya ta rufe iyakarta da Nijar sakamakon hambarar da Shugaba Mohamed Bazoum da sojojin kasar suka yi.
