News
An Yi Sulhu Tsakanin Abba Da Sheikh Daurawa
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf da Shugaban Hukumar Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa sun yi sulhu a tsakaninsu biyo bayan murabus din malamin daga shugabancin hukumar.
Wannan dai na zuwa ne bayan wata ganawar sirri da malamin ya yi da gwamnan a gidan gwamnatin jihar, a daren ranar Litinin.
Mataimakin Babban Kwamandan Hisbah, Sheikh Mujahid Aminudden, ya ce an yi sulhu tsakanin Sheikh Daurawa da gwamnan Jihar, Alhaji Abba Kabir Yusuf.
Sulhun ya gudana be karkashin jagorancin zauren malaman Kano da ma’aikatan hukumar Hisbah da kuma bangaren jami’an gwamnati.
Daga cikin wadanda suka halarci ganawar akwai, Sheikh Abdulwahab Abdallah, Farfesa Salisu Shehu, Farfesa Borodo, Dokta Sa’idu Dukawa, Dokta Mu’azzam Sulaiman Khalid da sauransu.
Wannan dai na zuwa ne bayan da Sheikh Daurawa ya yi murabus daga shugabancin Hisbah biyo bayan kalaman gwamnan jihar kan sukar ayyukan hukumar.
Kalaman gwamnan da suka sa Daurawa ya yi murabus sun jawo cece-kuce a jihar.
Murabus din Daurawa ta bar baya da kura, inda mutane suka dinga bayyana ra’ayinsu kan lamarin.
A gefe guda kuwa wasu kun yi kira da gwamnan ya bai wa malamin hakuri duba da irin yaki da baɗala da yake yi a jihar.
-
News2 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion6 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
