Connect with us

News

Babu barkewar cutar kyanda a Jihar Kano —Ma’aikatar Lafiya

Published

on

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Ma’aikatar Lafiya ta jihar Kano ta karyata labarin da wasu kafafen yada labarai suka buga na cewa an samu barkewar cutar kyanda a karamar hukumar birni da ke jihar, labarin da kafafen yada labarai na gida da waje suka yadawa.

Hakan na kunshe ne ta cikin wata Sanarwa da Jami’in Yada Labarai na Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano, Ibrahim Abdullahi, ya tura waJaridar Inda Ranka.

Jiragen Sama Biyu Sun Yi Karo Da Juna A Sararin Samaniyar Ƙasar Kenya

Sanarwar ta hakaito Darakta mai kula da cututtuka masu yaduwa, Dakta Imam Wada Bello, yana karyata labarin baki daya.

Dr. Imam ya yi nuni da cewa, kafin a ce an samu barkewar cuta akwai wasu matakai da alamomi da ake nazari a kan su tukuna da suka hada da binciken dakin gwaje-gwaje tare da tantance girmanta da adadin mutanen da suka kamu da ita.

Dangane da karamar hukumar Kano kuwa, a cewarsa, babu daya daga cikin hanyoyin da aka ambata da aka bi wajen tabbatar da barkewar cutar kyanda, inda ya bukaci jama’a da su yi watsi da labarin domin ba shi da kwararan hujjoji na harkar lafiya da za su tabbatar da shi.

Advertisement

Daraktan ya tabbatar da cewa ma’aikatar a fadake take yi a kan duk wata cuta da ke haifar da barna ga rayuwar al’umma ta hanyar daukar dukkan matakan da suka dace don dakile tasirin irin wadannan cututtuka.

Ya kuma ba da tabbacin cewa ma’aikatar tare da sassanta na kar-ta-kwana da na kananan hukumomi 44 (EPR) suna cikin shiri a kowane lokaci domin tunkarar barkewar cututtuka ba tare da bata lokaci ba tare da hadin gwiwar masu ruwa da tsaki.

Dakta Imam ya bayyana cewa, Tsarin Kula tare da Kai Dauki kan Barkewar Cututtuka (SORMAS), na kasa da ya nuna takaitaccen rahoton cutar kyanda a jihar Kano daga watan Janairu zuwa Maris 2024, ya nuna cewa akwai “zargin bullar cutar kyanda” har 697 a kananan hukumomi 23 a jihar Kano, inda karamar hukumar birni ke da adadin 647, ya kara da cewa an dauki samfura biyar don gwajin a dakin gwaje-gwaje kuma babu wanda ya nuna cutar kyanda ce.

Daraktan ya kara da cewa, karamar hukumar Kano ta zama karamar hukumar mai dauke da yawan wadanda ake “zargi” saboda kasantuwar asibitin yara na Hasiya Bayero a yankin, wanda ke matsayin cibiyar bincike da kula da cututtukan kananan yara da suka hada har da cutar kyanda a fadin jihar ba kawai a cikin karamar hukumar ba, yana mai jaddada cewa hakan ne ya mayar da asibitin jagora wajen samun rahoton bullar wadannan cututtuka a karamar hukumar idan aka kwatanta da sauran kananan hukumomi.

Da aka tuntubi shi, Jami’in Lafiya a Matakin Farko na karamar hukumar ta birni, Aliyu Jinjiri Kiru, wanda aka alakanta labarin da shi, ya ce babu inda ya taba yin wannan ikirari ba.

Ya jaddada cewa rahoton taronsu na sashin kar-ta-kwana ne sashin yada labarai na karamar hukumar ya fahimta ba daidai ba cewa an samu barkewar cutar kyanda a yankin.

Advertisement

Mista Kiru ya ce, abin da rahoton nasu ya kunsa shi ne ana ‘’zargin akwai cutar kyanda da mashako” a cibiyoyin kiwon lafiya da ke karamar hukumar ciki har da manyan asibitoci da nufin ankarar da masu ruwa da tsaki da su tallafa wa sashin wajen dakile lamarin idan har an tabbatar da hakan.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending