News
Shakara Biyu Da Rasuwar Tsohon Sakataren Kano Pillars Auwalu Zakirai
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
A ranar 10 ga watan Ramadan na shekarar 1443 rana ce da hantar al’ummar Musulumi ta kada, musamman kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars sauran wurare.
Labarin rasuwar Tsohon sakataren kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars kuma mafi dadewa a hukumar kwallon kafa ta jihar Kano, Alhaji Auwalu Musa Zakirai a ranar ta girgiza Al umma— daga mai istirja’i, sai mai hailala, sai mai zubar da hawaye, sai mai salati, sai mai yi masa addu’a.
Da Dumi-dumi: Majalisar Dattawa Ta Amince Da Kudirin Bai Wa Dalibai Rance A Matsayin Doka
Haka zalika , Alhaji Auwalu Musa Zakirai ya rasu yana da shekaru 70 a duniya.
Rahotanni na nuni da cewa ya rasu ne da safe a babban asibitin Muhammad Abdullahi Wase Kano bayan ya sha fama da jinya.
Marigayi Auwalu ya bar mata da ‘ya’ya 16 da jikoki da dama.
Marigayi Auwalu Zakirai ya kasance mai kula da harkokin wasanni wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen bunkasa harkar kwallon kafa a jihar Kano da ma kasa baki daya.
Mutuwar tasa dai ta zo ne a matsayin babban rashi ga hukumar kwallon kafa ta jihar Kano da daukacin ‘yan wasan kwallon kafa na jihar.
Marigayi Zakirai mutum mai tawali’u, mai gaskiya da kishin jihar da ba za a taba mantawa da sunansa ba a tarihin Kano.
Muna addu’ar Allah Madaukakin Sarki da ya gafarta masa dukkan kurakurensa, ya kuma sanya shi a Aljannar Firdausi.
