News
Shugaba Tinubu ya haramta wa ministoci da shugabannin hukumomin gwamnati tafiye-tafiye kasashen waje
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya bayar da umarnin hana duk wani tafiye-tafiyen da ministoci da sauran jami’an gwamnati ke yi zuwa kasashen waje.
Shugaba Tinubu ya ba da umarnin ne ta wata wasika da shugaban ma’aikatan fadar gwamnati, Femi Gbajabiamila, ya aike wa sakataren gwamnatin tarayya, George Akume.
A cikin wasikar, mai kwanan wata 12 ga Maris, 2024, Tinubu ya ba da umarnin hana duk wani tafiye-tafiye zuwa kasashen waje. Sai dai kuma za a iya amince wa wasu tafiyar idan ya zama dole wato “tafiya waɗanda ake ganin sun zama dole ayi su”.
Wani minista da ya bukaci a sakaya sunansa saboda ba shi da izinin yin magana a kan lamarin, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa shima ya samu kwafin wasikar daga fadar shugaban kasa.
A cikin wasikar, shugaba Tinubu ya bayyana damuwarsa kan dinbin kudaden da ake kashewa wajen wadannan tafiye-tafiye zuwa kasashen waje da jami’an gwamnati ke yi a cikin wannan mawuyacin hali na kokari da ake yi na ceto tattalin arzikin Najeriya da yake tangal-tangal.
Premium Times ta ruwaito cewa a dalilin wadannan matsaloli da ke kokarin kauda su, Ina mai sanar muku cewa shugaban kasa ya bada umarnin dakatar da duk wani tafiye-Tafiye zuwa kasashen waje daga yanzu.
Hakan ya biyo bayan kokari ne na rage kudin da ake facaka da su wajen irin wadannan tafiye tafiye.
Wasikar ta kara da cewa duk wani jami’in gwamnati da zai yi tafiya kasashen waje da dole ne ayi ta sai ya sami amincewar shugaban kasa kafin ya tafi, sannan kuma zai aika da bukatar haka makonni biyu kafin tafiyar kuma ya jira amincewa.
Idan ba a manta ba shugaba Tinubu ya bada irin wannan umarni tun abaya ne bayan dandazon jami’an gwamnati sama da 400 suka tafi taron COP28 a Dubai, lamarin da ya jawo cecekuce akai ganin halin matsi da yan najeriay ke fama da tun bayan cire tallafin mai da gwamnatin ta yi.
