Connect with us

News

Mahaifi Ya Sayar Da ‘Ya’yansa Guda 5 Naira Miliyan Daya Da Dubu Dari 2, A Jihar Sakkwato

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Yan sanda sun kama wani magidanci da ya sayar da ’ya’yansa biyar a kan kudin da bai kai Naira miliyan 1.2 ba a Jihar Sakkwato.

Advertisement

Dubun mutumin ta cika ne bayan da aka gano karin kananan yara 21 da wata ‘yar sanda mai safarar yara da kawarta suka sato daga Jihar Sakkwato suka kai su Abuja.

Majalisar Dattawa Ta Amince Da Karin  Albashin Alƙalai Sau Uku

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Ali Hayatu Kaigama, ya ce bayyana cewa bincike ya gano cewa magidancin, mazaunin unguwar Tudun Wada, ya sayar da kananan yara 28 ga wata ’yar sanda mai suna ASP Kulu Dogonyaro da abokiyarta Elizabeth

Advertisement

Aminiya ta ruwaito cewa Da yake holen wadanda ake zargin, kwamishinan ya bayyana cewa a cikin yaran da mutumin da ya sayar har da ’ya’yan cikinsa biyar, inda su ASP Kulu Dogonyaro suka biya shi tsakanin N150,000 zuwa N150,000 a kan kowane yaro.

 

Advertisement

Kwamishinan ya ce zuwa yanzu rundunar ta gano tare da ceto wasu yara 21 da barayin suka sato daga jihohi daban-daban.

 

Advertisement

Ya bayyana cewa barayin yaran suka yi safarar yaran ne ta hanyar yin sojan gona da cewa za su sama musu kyakkyawar kula a hannun kungiyoyi masu zaman kansu.

 

Advertisement

Daga Jaridar Aminiya

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending