News
Shugaba Tinubu Ya Fadi A Wurin Taron Ranar Dimokradiyya
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Wani faifan bidiyo da ya fara bazama a dandalin sada zumunta ya nuna yadda shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu, ya fadi bayan ya yi tuntuben sahu yayin da yake kokarin hawa bayan motar da zata zagaya da shi a filin taro na Eagle Square da ke Abuja.
Tinubu ya isa filin taro na Eagle Square tare da mai dakinsa, Sanata Remi Tinubu, domin shaida yadda bikin murnar ranar dimokradiyya ya ke gudana.
EDIL-KABIR: Gwamnatin Kano Ta Ba Da Hutu A Makarantun Firamare Dana Sakandire A Fadin Jahar.
Kafin zuwansa filin taron, shugaba Kasa Bola Ahmad Tinubu ya gabatar da jawabi ga ‘yan Najeriya Ranar Dimokradiyya
Ya iso filin taron kewaye da dakarun jami’an tsaro da ke gadinsa da kuma hadimansa ma
Tinubu, sanye da farar babbar riga da irin hularsa da kowa ya san shi da ita, ya yi kokarin rike karfe a jikin motar don kar ya kai kasa amma hakan bai kubutar da shi daga faduwa ba bayan ya yi tutuben sahu yayin hawa matakalar da ke bayan motar.
Nan da nan jami’an tsaronsa suka garzayo suka kawo masa agaji tare da taimaka masa wajen mikewa ya koma kan digadigansa.
Rahotanni na nuni da cewa A cikin faifan bidiyon, an ga shugaba Tinubu ya mirje, ya yi fuska, ya tsaya kyam tare da cigaba da dagawa jama’a hannu, alamar da ke nuna cewa karfinsa ya dawo jikinsa kuma yana cikin hayyacinsa.
An cigaba da fareti a filin taron yayin da motar da Shugaba Tinubu ya hau ta cigaba da tafiya a hankali, shi kuma ya cigaba da dagawa jama’a hannu.
-
News2 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
