Connect with us

News

Atiku Ya Jajantawa Shugaba Tinubu Bayan Da Yayi Kudungula A Cikin Motar Da Yake Kokarin Hawa

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Dan takarar da shugaba Tinubu ya kayar a zaɓen 2023, Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP, ya ce yana jajantawa Bola Tinubu dangane da zamewar da ya yi, a ranar Laraba.

Ina matukar jajantawa shugaba Bola Tinubu dangane da ɗan hatsarin da ya samu a lokacin da yake ƙoƙarin zagaya masu fareti na bikin ranar dimokuraɗiyya.

Shugaba Tinubu Ya Fadi A Wurin Taron Ranar Dimokradiyya

“Ina fatan dai lafiya lau” in ji Atiku.

A baya-bayan nan dai an ga yadda tsohon mataimakin shugaban ƙasar, Atiku Abubakar ke ƙara ƙaimi wajen yin hamayya ta fuskar sukan abubuwan da yake ganin gwamnatin shugaba Tinubu ba ta yi daidai ba, kamar yadda jaridar BBC Hausa ta bayyana.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending