Connect with us

News

Yaran Masu Faɗa Aji Ne Kaɗai Zasu Iya Samun Lamunin Karatu Da Gwamnatin Tarayya Za Ta Bayar —BUK Lecturer

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Dokta Sa’id Ahmad Dukawa babban malami a sashin nazarin kimiyyar siyasa a Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK) ya bayyana cewa ‘ya’yan manya ne kadai zasu  iya samun lamunin karatu da Gwamnatin Tarayya za ta bayar.

Advertisement

Jaridar DAILY TRUST ta ruwaito cewa Dokta Sa’id Ahmad Dukawa ya kasancewar sa Manazarcin kan al’amuran yau da kullum ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida a wani taron da kungiyar FRAME Democracy Team ta shirya.

Addu’ar Mutane Ce Ta Taimaka Wajan Kare Jihar Daga Bullar Cutar kwalara —Gwamnatin Kano

Shirin da Gatefield Impact ta yi na inganta fahimtar jama’a game da yanayin Dimokuradiyya a Najeriya da ya gudana a cikin BUK.

Advertisement

Ya ce “Kalubalan da ake fuskanta a yanzu shine waɗanda suka kasance matasa ne kuma suka samu damar rike mukamai a Gwamnatance a shekarun da suka gabata.

Su ne ke toshe duk wata dama ga matasa, ciki har da kyautar guraben karatu wato (Scholarship), dukkansu sun ci gajiyar tallafin karatu na Gwamnati a kyauta, amma a yanzu sun bullo da tsauraran sharudda na rancen kuɗi ga dalibai wanda ’ya’yan jiga-jigai ne kawai za su iya cika wannan sharaɗin, wanda hakan yana nufin mafi yawan ƴaƴan talakawa za su kare rayuwar su suna yawo kan tituna ba tare da samun ilimi ba”

Advertisement

Ya kuma buƙaci matasan Najeriya da su kasance masu gaskiya kuma su kasance da tunanin samar da ci gaba, kuma ku kasance a shirye wajen gyara kuskure ko da sun kai ga mukamai.

Shirin wanda aka shirya domin murnar cika shekaru 25 na mulkin dimokuradiyyar Najeriya ya tattauna kan muhimmancin dimokuradiyya da kuma abubuwan da suka shafi kama-karya a kasar.

Advertisement

Tun da farko Mahmud Jafar wanda shine Manajan Shirin FRAME ya bude taron da yin nazari kan tafiyar Dimokuraɗiyyar Najeriya tsawon shekaru 25 da suka gabata zuwa yanzu.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending