News
Innalillahi Wa”inna Ilaihi Rajiun Allah Yayiwa Tsohuwar Shugabar Mata Ta PDP Ta Kasa, Hadiza Adado Rasu
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Tsohuwar shugabar mata ta jam’iyyar PDP ta kasa Hajiya Hadiza Adado ta rasu.
A cewar sanarwar maigidanta, Alhaji Yusuf Adado ya ce marigayiya Hadiza ta rasu ne a daren Laraba bayan gajeruwar rashin lafiya, a Kano.
Sanarwar ta ce za a yi jana’izar ta a safiyar ranar Alhamis.
An gudanar da Sallar jana’izar a kusa da zagayen Triumph da ke Wapa a karamar hukumar Fagge a jihar Kano.
Rahotanni na nuni da cewa ta ruwaito cewa ta bar mijinta da ‘ya’ya hudu da kuma ‘yan uwa da dama.
Advertisements
