Entertainment
Tattaunawar jaruma Hadiza Gabon ta janyo cece-kuce
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Ana cigaba da cece-kuce a dandalin sada zumunta, akan batun tattaunawar da jarumar masana’antar shirya finafinan Kannywood, Hadiza Gabon, ke gudanarwa a shafin YouTube.
Anda take gayyato abokan sana’ar ta, tare da yi musu tambayoyi masu zafi, wadanda wasu ganin tambayoyin sun fita daga kwarewar aikin jarida, don kuwa akwai wata jaruma da har sai da ta zubda hawaye a dalilin tambayoyin nata.
Babbar magana: waliyin amarya ya sace sadaki ana tsaka da daurin aure a Kano.
Hadiza Gabon ta sanyawa shirin ta suna “Gabon’s Room Talk Show” wanda a baya bayan nan ta tattauna da mawaƙi El-Mu’az, tayi masa tambaya akan alaƙarsa da wata abokiyar sana’arsu, lamarin da ya fusata mawaƙin, har shima ya jefa mata wasu tambaya akan sana’ar da ta keyi da kuma yadda take samun kuɗi.
Marubuta a shafin Facebook na cigaba da bayyana ra’ayoyinsu akan batun, inda mafi yawa ke sukar tsarin da jaruma Hadiza Gabon ke bi wajen yin tambayoyi ga baƙin ta, harma wasu na ganin ya kamata ta nemo kwarewar aikin jarida, domin tattaunawar ba iya ita kadai da baƙin ta ke gani ba, Duniya ce ke kallon su.
-
News6 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News4 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News6 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
