News
Ƴan bindiga sun karbi kudin fansa sunƙi bayar da gawar Sarkin Gobir
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Masarautar Sabon Birnin Gobir a jihar Sakkwato ta tabbatar sako ɗan marigayi Sarkin Gobir Alhaji Muhammad Bawa Isa da aka sace su tare mai suna Kabir.
Wani mai magana da yawun masarautar Alhaji Shuaibu Gwanda Gobir ya ce an sako shi ne da daren jiya bayan biyan waɗanda suka yi garkuwa da shi da Masarautarkuma mahaifinsa kuɗin fansar da suka bukata, amma sun ƙi bayar da gawar mahaifinsa inda suka ce sun riga sun binne shi.
Yanzu haka dai ɗan nasa na can na karɓar magani a asibiti a birnin Sakkwato. Magajin Garin na Sabon Birni ya Kuma yace za su yi wa marigayi Sarkin Gobir jana’iza daga nesa wato salatul Ga’ib a yau.
Ya buƙaci al’ummar Musulmi a duk duniya da su bi sawunsu wajen yi masa sallar wadda ya ce za su yau.
Idan ba,amantaba jaridar Inda ranka ta rawaito cewa Yan bindinga sunyi garkuwa da Sarkin Gobir dashi da Dansa wanda shine Direban da yake Jan motar Sarkin a lokacin, bayan wani taro daya raka mahaifinnasu.
-
News2 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion6 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
